Yusuf Magaji Bichi: Abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon shugaban DSS da ake cece-kuce akan sa

Spread the love

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta ce sabon jagoran hukumar ya sami horo a bangarorin leken asiri da bincike da bayar da kariya da kuma tattara bayanai.

Yan Nijeriya na korafi game da nadin sabon shugaban hukumar tsaro ta cikin gida da shugaba Muhammadu Buhari yayi ranar alhamis.

A cikin takardar sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya fitar, Yusuf Magaji Bichi zai maye gurbin Lawal Daura a hukumar.

Nadin  dai ya jawo cece-kuce a dandalin sadarwa inda wasu ke ganin shugaban ya nuna wariya na nada dan arewa a madadin Mathew Seifeyela dake rikon kwarya na shugabantar hukumar.

Wasu na zargin shugaban da tada lamarin dake zaune ganin cewa Yusuf Magaji Bichi yayi ritaya daga aiki cikin watan Febreru na wannan shekarar bayan shafe tsawon shekaru talatin da biyar yana aiki.

Ga wasu daga cikin abubuwamn  da ya kamata ku sani game da sabon shugaban hukumar kamar haka:

Ya yi makarantar sakandaren Dambatta a Kano, sannan ya halarci kwalejin share fagen shiga jami'a ta Kano, ya kuma karanci kimiyyar siyasa a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Yusuf Bichi ya taba zama daraktan hukumar ta DSS a jihohin Jigawa da Niger da Sokoto da Abia.

Sanarwar da Garba Shehu ya fitar ta ce sabon jagoran hukumar ya sami horo a bangarorin leken asiri da bincike da bayar da kariya da kuma tattara bayanai.

Ya yi kwasa-kwasai a Birtaniya da kuma Najeriya, sannan ya rike mukamai da dama a hukumar ta 'yan sandan ciki ta kasar.

Sabon shugaban hukumar  ya fara aikin tsaro a ofishin gwamnatin Kano, daga nan kuma sai ya shiga hukumar 'yan sandan ciki ta Najeriya (NSO), sannan ya zama mai shigar da kara a hukumar DSS.

Yayi murabus daga aiki a karo na farko cikin shekarar 2017 bayan ya rike mukamin daraktan kudi da kulawa na hukumar. Tsohon shugaban  hukumar ya sake dawo dashi aiki inda yayi watanni kalilan gabanin sake yin murabus a cikin watan febreru na bana.

Leave a Response